Labarai

Yarjejeniyar yin kamfanin Madara tsakanin Kaduna da Denmark zai samar da ayyukan yi 50,000

Gwamnatin jihar Kaduna da kamfanin Arla Foods International, sun kulla yarjejeniya domin kirkirar kamfanin Madara a jihar Kaduna.

Kulla yarjejeniyar sai zamar da jihar Kaduna zama jihar da ta fi kowacce a Najeriya samar da Madara tare da samar da ayyukanyi 50,000 da zarar an fara aikin.

Mataimakin shugaban kamfanin Arla, Steen Hadsbjerg, ne ya bayyana haka yayin kulla yarjejeniyar.

Ya kuma kara da cewa kamfanin zai juba hannun jarinshi na Euro miliyan 100 kwatankwacin N40,02,54,37,500.00. (Biliyan Arba’in da miliyan miliyan ashirin da biyar da dubu dari hudu da talatin da bakwai da dari biyar.