Kasar Indiya ta cika shekara 74 da samun ‘yancin Kai, shekara 13 a gaban Najeriya

Karatun minti 1

Ranar 15 ga Agusta kowacce shekara, rana ce da kasar Indiya ke murnar samun ‘yancin Kai daga turawan mulkin mallaka na kasar Burtaniya.

A yau 15 ga Agusta 2020, kasar take cika shekara 74 da samun ‘yancin kai, shekaru 13 tsakanin kasar da kuma Najeriya.

DABO FM ta tattara cewa da yawa wasu daga al’ummar Najeriya suna sanya kasashen Indiya da Brazil a matsayin kasashen da suka samu ‘yancin kai a tare. Wannan sam ba gaskiya bane.

A jawabin murnanr da Firaministan kasar, Narendra Modi ya jadadda aniyar gwamnatinshi na yaki da cutar Korona, ya bayyana cewa tuni kasar Indiya tayi nisa wajen gwaje-gwajen sanar da maganin Korona guda 3.

Kazalika ya ce gwamnatinsa ta yi kokari wajen sadar da mata marasa hali ga audugar mata sama da miliyan 50 a kan kudi Rupee 1 kacal, kwatankwacin N5.

DABO FM ta tattara cewa ana nuna murnar samun ‘yanci a kasar ta hanyoyi da kowacce kasa take yi, sai dai ‘yan kasar da shuwagabanni su kan harba jirgin leda a gidajensu.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog