Sabon Gwamnan jihar Borno bai iske ma’aikaci ko guda 1 ba, a ziyararshi zuwa babbar sakatariya a Maiduguri

Sabon gwamnan jihar Borno Engr Babagana Umara Zulum ya bayyana rashin jin dadinshi bisa rashin iske ma’aikata a babbar sakatariyar jihar Borno a lokacin da ya kai ziyarar bazata zuwa sakatariyar a safiyar Juma’a.

Gwamnan ya koka tare da nuna rashin jin dadinshi ga lamarin.

“A safiyar yau, na kai ziyara babbar sakatariya jihar nan, ya iske dukkanin ofisosin ma’aikata a rufe.”

Zulum yace duk da cewa lokacin azumi ne, amma duk da haka ko kaso 2 daga 100 na ma’aikatan basu fito aiki ba.

“Duk da lokacin azumin Ramadan ne, amma ko kaso 2 cikin 100 na ma’aikata basu fito aiki ba.”

Gwamnan ya bada tabbacin daukar babban mataki tare da tabbatar da bin doka ga dukkanin ma’aikatan jihar Borno domin cigaban jihar baki daya.

Early this morning, I had an assessment tour at the state secretariat and virtually met all offices empty, I am aware that it is Ramadan period, but atleast out of 100%, 2% cannot come to work. We will surely look into this and ensure discipline.

Posted by Engr Babagana Umara Zulum on Friday, May 31, 2019
%d bloggers like this: