Labarai

Tsananin kishi ya sanya wata mata cinnawa kanta wuta

Tsananin kishi ya sanya wata baiwar Allah mai suna Rabi, kona kanta bayan mai gidanta ya karo mata kishi, inda tace ga garinku nan.

Lamarin da ya faru a unguwar Gayawa dake karamar hukumar Ungogo dake jihar Kano.

Gidan Rediyon Freedom dake Kano ya tattara cewar a kwanakin baya ne mai gidan Hajiya Rabi, mai suna Badamasi ya kara aure, lamarin da ya sanya uwar gidan ta kasa jurewa.

Tini dai rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al’amarin ta hannun kakakinta, DSP Haruna Abdullahi.

Rundunar tace ta dauki gawar Haj Rabi tin kwanaki 3 da faruwar al’amarin wanda ya tabbatar da hukumar tana cigaba da bincike.

A nasu banagren, yan uwan mamaciyar, sun bayyana rashin jin dadinsu bisa ga ta’asar da ‘yar uwar tasu ta aikatawa kanta.

Haka zalika a banagren dangin mijin matar, Salisu Safiyanu, ya shaidawa Freedom cewar lallai ya firgece a dai dai lokacin da ya ga rabin gawar matar dan uwan nashi a kone a sa’i’lin da ya shiga gidanta.

Sai dai har yan rundunar yan sanda bata lamunce wani daga cikin danginta ya ga gawar ba bisa binciken da hukumar take yi.

A wani labarin, a jihar Bauchi, wani saurayi ya caccakawa budurwarshi mai suna Patience a gadon baya lamarin da yayi sanadiyyar barinta duniya.

Duk dai a irin wannan, wata baiwar Allah ya jihar Katsina kuwa, daba wa mai gidanta wuka tayi shima da yayi sanadiyyar zuwanshi lahira.

Masu Alaka

An fara gano dattawan dake zancen batsa da matar data caccakawa mijinta wuka

Dabo Online

Maryam Sanda ta tsere bayan Kotu ta tabbatar da kisan da tayi wa mijinta

Dabo Online

Kotu ta bayar da belin Matar da ake zargi da caccakawa Mijinta wuka

Dabo Online

‘Ungozoma’ ta yanke wa mijinta Harshe da Hanci, ta kira Surukarta ta dauki gawa

Dabo Online

Bayelsa: Mata ta kwararawa mijinta tafasasshen ruwa saboda ya je daukota da wuri

Dabo Online

Hoto mai dishi-dishi na ‘@Habib4u’ mai tarayya da Hanan da ake zargin ta caccakawa mijinta wuka

Dabo Online
UA-131299779-2