//

Yanzu-yanzu: Baza mu yarda da hukuncin kisa ba, zamu daukaka kara -Lauyoyin Maryam Sanda

0

Da alama tsuguni bata kare ba, lauyoyin Maryam Sanda wadda alkalin kotun tarayya dake Abuja, jastis Yusuf Halilu ya yankewa hukuncin kisa sunce zasu daukaka kara domin basu yarda da hukuncin da ya yanke ba.

Majiyar Dabo FM ta rawaito daya daga cikin lauyoyin ya bayyana cewa “Tasarin mulki ya bawa Maryam Sanda damar daukaka kara, kuma lallai zamu daukaka kara.” Kamar yadda jaridar Legit.Ng ta fitar da sanyin safiyar Laraba.

Wannan yazo ne bayan yanke hukuncin kisa da kotu tayi a ranar 27 ga Junairu, wanda kotu ta sami wadda ake zargin da kashe mijinta, Bilyaminu Bello a ranar 19 ga Nuwanba 2017.

Masu Alaƙa  Lauya ya kai gwamnatin Najeriya Kotu bisa bukatar cire rubutun Ajami daga jikin Naira

Alkali jastis Yusuf Halilu ya bayyana kotun tayi amfani ne da sashi na 221 domin yanke mata hukuncin.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020