Labarai

Kiwon Lafiya: Riga Kafi ko shan magani? Zabi daya don kula da lafiyar Jiki


Idan ana maganar kula da lafiyar jiki, to ababe biyu ne suke tasowa; ko dai ayi riga-kafi, ko kuma shan magani.

Kowa dai ya san yanda ake yi wa Riga-kafi taken ya fi magani. Kuma riga-kafin nan ba wai ana nufin irin allurori da ake wa yara kawai ba ne, ko kwayoyi da ake sha da sauransu.

Manyan mutane ma za su iya yin riga-kafi ta fuskoki da dama, wanda idan an ingantasu, to jinyar ma ba lalle ne ta kama mutum ba.

Misali akwai riga-kafin kula da shi kansa tunani(kwakwalwa), gangar jiki, cikin jiki, garkuwar jiki, da sauran wasu surorin jiki.
Riga-kafin tunani da yake damfare da kwakwalwa, zai bayu ne na daga yanda mutum yake tafikar da nazarinsa, tunaninsa, da sauransu.

Tunani da nazari mai dauke da damuwa, fargaba, zullumi, rashin tabbas, to shine yake haifar da matsalolin da za su iya kawo matsala ga kwakwalwa. Bugu da kari, irin abin da mutum zai ci ko sha, da yanayin da yake zaune, duk za su iya zama riga-kafi ga mutum ta yanda kwakwalwarsa ba za ta samu matsala ba, har tunaninsa ya shiga wani yanayi, ana batun mutum ya samu matsala.

Sauran riga-kafin da na lissafo na jiki da gangar ciki, su ma hakan suke. Don kuwa abin ci, abin sha, muhalli, yanayin nutsuwa da tunani, duk suna da tasiri wajen samun lafiyar jiki. Kun ga kenan kula da su din sosai, zai iya zama riga-kafi ta yanda mutum zai kare jikinsa da ga kamuwa da cuta.

A misalance, motsa jiki, da cin kayan ganye(salak, kabeji, allaiyahu, da su zogale da danginsu) na taimakawa sosai wajen kare mutum daga kamuwa daga hawan jini da su ciwon zuciya. Kun ga kenan cin su, da kula da motsin jikin ya zama riga-kafi kenan.

Idan kuwa har hakane, riga-kafi ya fi sauki, alfanu da kuma muhimmanci akan mutum wajen kula da jikinsa, kafin cuta ta kamashi ya shiga damuwa, zullumi, kashe kudi, wata kila a mutu.

Karin Labarai

Masu Alaka

Hanyoyin kaucewa matsanancin warin baki

Dabo Online

Kiwon Lafiya: Mutane masu kiba sunfi amfanuwa wajen warkewa daga ciwon..

Hassan M. Ringim

Kiwon Lafiya: Mata suna gane namiji mai karyar Ido na ganin Ido – Binciken Kwakwalwar

Dangalan Muhammad Aliyu

Agwaluma na rage karfin maza -Binciken Masana daga Jami’ar Madonna

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu babu cutar ‘Polio’ a Najeriya – WHO

Dabo Online

Cin Nama yana kara yawaitar wari a jikin ‘Dan Adam – Masana

Dabo Online
UA-131299779-2