//
Wednesday, April 1

Kotu ta kori bukatar haramtawa Ibrahim Magu zama shugaban EFCC

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Ranar laraba wata babbar kotun Abuja ta tabbatar da cewar Ibrahim Magu zai ci gaba da kasancewa shugaban rikon kwarya na hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Hukuncin da aka zartar a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, mai shari’ah Ifeoma Ojukwu ta bayyana cewar bukatar masu karar ba mai karbuwa ba ce, ba ta da nagarta, don haka ta kori karar.

Bukatar da aka turawa kotun tun da farko, ta samo asali ne saboda majalissar dattawa ta 8 karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki, ta kasa tantance Magu gami da tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar mai cikakken iko.

Masu Alaƙa  Gwamnoni zasu fidda mutane miliyan 24 daga Talauci zuwa shekarar 2030

Hakan ya bayu ne sanadin matsalar da aka samu wajen tantance Magu daga bangaren hukumar tsaro ta farin kaya, yanda suka turo wasiku har biyu masu cin karo da juna, wanda duk tsohon shugaban hukumar Lawal Daura ya rattabawa hannu.

A yanzu dai za a iya cewa Magu zai ci gaba da jagorantar hukumar da sunan shugaban rikon kwarya, har zuwa lokacin da wannan majalissa ta 9 za ta tantanceshi idan an tura musu da wannan bukatar daga fadar shugaban kasa.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020