/

Ko kasan Victor Odungide, Wanda yayi iƙirarin kashe shugaba Buhari idan har ya zarce?

Karatun minti 1

A kwanakin bayan gaf da gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya, wani matashi mai suna Victor Odungide yayi furucin da yayi nuni da son ya kashe shugaba Muhammadu Buhari.

Victor yayi wannan furuci ne daidai lokacin da  shugaba Buhari ya wallafa wani sako a shafinshi na Twitter, inda yake bayyanawa al’ummar Najeriya cewa bazai raba kudi daga asusun kasar ba domin yakin neman zabe.

Tin a lokacin da Victor yayi wannan furuci, kamfanin na Twitter suka dakatar dashi domin ya saba ka’idar ta kamfanin ya gindaya nayi barazanar rai ga wani mai amfani da manhajin.

Bayan bincike da wakilanmu suka gudanar, mun gano cewa Victor ya bude sabon account na twitter da suna mai suna @Victor_odungide, wanda har mukayi kokarin jin matsayarshi akan batun kisa shugaba Muhammadu Buhari.

Sai dai har lokacin da muka hada wannan rahotan, kimanin awanni biyar bai bamu amsa ba.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog