Copyrighted.com Registered & Protected

Daga kin gaskiya: Matashin daya sha ruwan kwata akan Buhari bai mutu ba.

Matashin daya sha ruwan kwata domin nuna farinciki ga nasarar shugaba Muhammadu Buhari bai mutu ba.

Wasu daga cikin manyan shafunan yada labarai a Najeriya irinsu Legit Ng da The Guardian tare damu DaboFM, duk an wallafa labarin mutuwar matashin.

Saidai bayan binciken da editan jaridar Leadership Hausa, Sulaiman Bala Idris ya gudanar yace wakilinsu ya gana da matashin inda ya tabbatar masa yana nan a raye cikin koshin lafiya.

Matashin mai suna Aliyu Muhammad Sani dan asalin jihar Bauchi, yana sana’ar yin fenti.

“Yanzu haka kana magana dani ina kan hanyata ta zuwa garin Bauchi bayan na kammala aiki na na fenti.” – Aliyu

Masu Alaƙa  Abuja: Malam Shekarau ya karbi shedar zama sanatan Kano ta Tsakiya daga INEC

 

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: