Labarai

Komawa ga Allah ne mafita a halin da Najeriya ke ciki – Sheikh Rabi’u Zariya

Yin hakuri da soyayyar juna, shi ne kan gaba a turbar wanzar da zama tare da kawo ci gaba a kasa.

Shugaban Kungiyar Fityanul Islam ta Jihar Kaduna, kuma Shugaban gamayyar Kungiyar wanzar da zaman lafiya da hadin kan Al’ummar musulmi na jihar Kaduna, Sheikh Rabi’u Abdullahi Zaria, ya bayyana hakan, da yake tsokaci game da ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin wai-waye akan wanzar da zaman lafiya a kowacce ranar 21 ga watan Satumbar kowacce shekara.

Ya ce, tunda Allah ya hada Al’ummomi iri daban-daban masu addinai daban-daban, ya zama wajibi a hada kai domin kawo ci gaba da tabbatuwar samun rayuwa mai kyau.

Ya kara da jaddada muhinmancin watsi da yada jita-jita, Wanda ya ce, shi ma na taka rawa wurin samar da matsala a lokutan da aka samu rashin fahimta.

Da ya juya ga kungiyoyin addinai kuwa, ya naime su da ci gaba da kokarin da suke a ko da yaushe, na shirya taruka da wa’azuzzuka na zaman lafiya tsakanin mabiyan su.

Ya naime matakan gwamnati Uku, da suka hada da gwamnatin tarayya da Jihohi da kuma kananan hukumomi, su samar da ayyukan yi ga al’umma, Wanda a cewar shi, hakan, zai taimaka wurin rage zaman banza da tashe-tashen hankulan da ake samu tsakanin matasa a yau.

“Lallai ne kuma, masu hannu da shuni su samar da kamfanoni da kananan masana’antu da kuma samar da jari mai sauki, domin rage zaman kashe wando da ke tsakanin matasa” inji Sheikh Rabi’u Abdullahi.

Daga karshe, ya rufe da Addu’an Allah ya kawo dawamammen zaman lafiya a kasa baki daya.

Comment here