//
Wednesday, April 1

Kaduna: Rusau da gwamna El-Rufa’i zai yi a kasuwar Sabon Gari bazata shafi ‘Yan Kasuwa ba

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Zariya, Kaduna State: Saboda bayar da wa’adin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi a makon da ya gabata ga wadanda ke da gine–gine a zagaye da kasuwar Sabon garin
Zariya, na su tashi, domin rushe gine – ginen, ya sa an sami zantuka
da dama daga wasu ‘yan kasuwa.

Binciken da wakilinm DABO FM ya gudanar, ya gano cewar, wa’adin da gwamnatin jihar Kaduna ta ba wadanda aka ambata, tun a watannin baya an biya su diyyar gine–ginensu, amma ba su tashi ba.

Sai dai a wannan lokacin ne gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umurnin kwanaki 7 daga ranar 17 zuwa 24 ga wannan wata na
Satumbar wannan shekara ta 2019, da su bar harabar wadannan gine–gine da suka zagaye kasuwar Sabon garin.

Masu Alaƙa  Yadda Hakimin Birnin Gwari ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane suna tsaka da barci

Wannan sanarwar da gwamnatin jihar Kaduna ta bayar mai dauke da sa hannun manajan shiyya ta daya na hukumar kula da tsara birane ta jihar Kaduna ‘KASUPDA’, ya bayar da dama ga wasu da suke yada jita–jitar cewar wannan wa’adi, daukacin ‘yan kasuwar Sabon gari aka bawa har wadanda da suke gudanar da harkar kasuwanci a wannan kasuwa.

Wakilinmu da ke Zariya ya sami damar zantawa da shugaban qungiyar ‘yan kasuwar Sabon garin Alhaji Ibrahim Mai Gwal, inda ya tabbatar da cewar, wannan wa’adi, bai shafi ‘yan kasuwar da suke cikin kasuwar ba,
ya dai shafi ‘yan kasuwan da suke cikin gine–ginen da gwamnatin jihar Kaduna ta ba su wa’adi ne kawai.

Masu Alaƙa  Babban shehin malamin coci ya samu wahayin El-Rufa'i bazai taba mulkin Najeriya ba

Alhaji Ibrahim Mai Gwal, ya kammala da kira ga daukacin ‘yan kasuwan da suke kasuwar Sabon Garin Zariya, da su riqa yin taka tsan–tsan da ma su yada jita-jita a kan wannan takarda da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar ga wadanda ta biya su diyya, da suka mallaki gidajen da suka zagaye wannan kasuwa.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020