(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Kotu ta daure babban jami’in INEC shekaru 6 bisa hannu a cikin karbar cin hancin miliyan 45

dakikun karantawa

Kotu ta daure wani mataimakin darakta a Hukumar zabe ta INEC, Auwal Jibrin, har tsawon shekaru 6, bisa karbar cin hanci daga tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison Madueke.

Hukuncin ya daurin ya zo ne bayan da hukumar EFFC ta bukaci yin haka a ranar Juma’a 28 ga watan Yuli ta hannun lauyan ta.

EFFC ta kara tasa keyar Garba Ismails a gaban mai shari’a Yusuf Birnin Kudu dake a jigawa a wata babbar kotu dake garin Gumel, akan laifi guda 6 cikin harda samun kudade ta haramtacciyar hanya.

EFFC ta ce kafin shigar da su gaban kuliya, ta samu bayanai da suka nuna cewa sun amfana daga cikin $115,010,000 na Alison Madueke, wanda aka raba lokacin zaben 2015.

Bincike ya nuna cewa sun samu Naira miliyan 45 daga cikin miliyan 250 da aka kai jihar Jigawa domin chanza akalar zaben 2015.

EFCC tace jami’an basu amsa laifin su ba a farko, hakan yasa aka shiga shari’a mai tsawo kafin daga bisani aka kawo shaidu 5 da hujjoji 20 domin tabbatar da zargin da ake musu.

Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Yusuf Birnin Kudu ya bayyana cewa; “Dukkanin Hujjojin da shedu da aka gabatar sun wuce ayi kokwanto. An karbi dukkanin hujjoji da masu kara suka gabatar.”

KOTun ta kara da cewa, wadanda ake karewa sun kasa kawo gamsassun hujjojin da zasu warware hujjojin masu kara, a saboda haka, an tabbatar da laifi akan wandanda ake zargi.

DAGa nan ne lauyan EFCC, Gambo Muhammad, ya bukaci kotun data daure su bisa hukuncin sabon da suka aikata.

Lauyan wanda akai kara na biyu, Garba Ismaila, ya roki alfarmar kotun data sassauta masa hukuncin da zata yanke na zaman gidan kason.

KOtu ta daure mai laifi na farko, zaman gidan yari, shekara 7 babu zabin tara. Inda kuma ta yankewa mai laifi na 2(Mataimakin Daraktan hukumar INEC) hukunci zaman gidan yari na shekara 6.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog