Labarai

Shugaba Buhari ya nuna alhininshi ga mutuwar Umar Sa’idu Tudun Wada

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana alhinin rashin fitaccen dan jarida, Alhaji Umaru Sa’idu Tudun Wada.

Shugaban ya aike da sakon ne ta hannun mai magana da yawunshi, Mallam Garba Shehu.

SHugaba Buhari ya bayyana Malam Sai’id Tudun Wada a matsayin mutum kamilalle wanda yake aiki tukuru ga Najeriya ta fannin aikin jarida.

“Aikin jarida aiki ne da yake zamewa al’umma mudubin dubawa wanda yake haska musu abinda shugabanninsu sukeyi. Ina alfahari da yacce marigari Umaru Tudun Wada ya taka rawa a fanninshi.

“Inaso inyi amfani da wannan dama domin aike sakon ta’aziyya ga kungiyar mawallafa ta Najeriya, gwamnatin jihar Kano da dangin Alh Tudun Wada. Allah Ya basu hakurin jurewa shi kuma Yayi masa sakayya da gidan aljanna.

Malam Umar Tudun Wada ya rasu a ranar Lahadi, 30 ga watan Yulin 2019 sakamakon hatsari daya rutsa dashi a kan hanyarshi da komawa garin Kano daga babban birnin tarayyar Abuja.

Tin bayan fara aikin jaridarshi a gidan Talbijin na CTV dake Kano a shekarar 1981, Marigayi Alaji Umaru Tudu Wada, ya rike shugaban gidan rediyon jihar Kano (Radio Kano) da gidan rediyon Freedom. Ya kuma yi mai bawa tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso, shawara a fannin yada labarai.

Karin Labarai

Masu Alaka

Tinda China da Indiya suka cigaba, babu abinda zai hana Najeriya ci gaba – Buhari

Dabo Online

APC ce ta lashe zaben Kano kuma ta tabbatarwa Kotu – Buhari

Dabo Online

Duk da zaman Kotun da ake yi a yau, a kan shari’ar shugaban kasa

Rilwanu A. Shehu

Zuwan Buhari Kano: Shin Buhari yana goyon bayan ‘yan rashawa?

Dangalan Muhammad Aliyu

Aisha Buhari ta yiwa Mamman Daura da Garba Shehu kaca-kaca a Villa

Muhammad Isma’il Makama

Mun dauki niyyar fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 100 daga bakin Talauci a shekaru 10 masu zuwa

Dabo Online
UA-131299779-2