Manyan bukatu 5 da Ganduje yake so majalisa ta zartar masa kan masarautar Kano

A wani bincike na Dabo FM, Daily Nigerian tayi ido biyu da ita wannan sabuwar doka mai cike da bukatun Gwamna Ganduje, wadannan sune jerin manyan abubuwa biyar da zasu faru idan dokar ta samu sahalewa.

1-Gwamna shi ke damar nada Manyan hakimai masu zabar Sarki.
Gwamna zai iya tsige masu zaben Sarki a duk sanda ya ga dama ya nada wanda yake so kuma su jagoranci nadi ko tsige sarkin da gwamnan baya so.

2- Gwamna shine wanda zai tabbatar da kasafin kudin Masarautu.

3-Gwamna yana damar dagawa ko rage darajar Sarki.

4-Gwamna yana da cikakken ikon nadawa ko sauke Sarki a duk lokacin da ya yi niyyar yin haka.

Masu Alaƙa  Kano: Cin Hanci: Ganduje ya rabawa wasu ma'aitakan INEC filaye

5-Za a iya cire Sarki idan ya jera lokuta uku a jere baya halartar taron sarakuna da gwamnati.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.