Siyasa

Mulkin Adamawa ya bani wahala, Ina roko a yafe min – Bindow

Gwamnan jihar Adamawa, Muhammad JIbrilla Bindo ya bayyana jagorancin jihar a matsayin aiki mai tsaurin gaske, inda ya kuma bayyana cewa yana da yakinin ya batawa wasu rai don haka yake neman yafiya a wajen su.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa gwamnan yayi wannan jawabi ne a wani taro da yayi kama da na bankwana a garin Yola, Bindow ya nemi wadanda ya batawa dasu yafe masa musamman a cikin watan Ramadan da ake ciki.


A taron da aka gudanar a babban dakin taro dake gidan gwamnatin jihar dake Yola, Bindow ya kaddamar da shirin Inshorar lafiya.
“Sanin kowa ne, jihar Adamawa akwai kalubale. Jagorancin akwai wahala, sai dai nayi iya bakin kokari a shekarun da suka wuce.


Gwamnan ya kara da cewa; daga cikin abinda zai yi kewa bayan barinshi mulki shine rabuwar shi da mataimakin gwamnan jihar Martins Babale.
“Ya zame min ‘dan uwa nagari wanda na karu a zamana dashi, mutum ne mai kwazo da aiki nagari.

Karin Labarai

Masu Alaka

Adamawa: Ganduje, El- Rufa’i na shirin kawo ‘Yan Sara-Suka domin tafka magudi – PDP

Dabo Online

Zaben2019: INEC ta dage zabe a jihar Adamawa bisa mutuwar ‘dan takara

Dabo Online

Kotu ta kwace zaben ‘Yan Majalissun jiha guda 2 daga APC ta baiwa PDP a jihar Adamawa

Dabo Online

Adamawa: Fintiri ya kwace filayen makaratu da aka rabawa wasu shafaffu da mai

Dabo Online

Adamawa: Fintiri na jami’iyyar PDP ya lashe zaben Gwamnan Adamawa

Zaben Gwamna: Gwamnan jihar Adamawa ya fadi akwatin gidan gwamnati

Dabo Online
UA-131299779-2