Labarai

Kotu ta umarci Buhari ya kwato Kudaden fansho da tsofaffin Gwamnonin da suka zama Ministoci da Sanatoci


Wata babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a jihar Lagos, ta umarci gwamnatin tarayya da tayi amfani da ikonta wajen ganin ta karbo dukkanin makudan kudaden da tsofaffin gwamnonin kasar suke karba da sunan kudin fansho.

A lokacin da ta ke yanke hukunci, mai shari’ah Oluremi Oguntoyinbo, ta bukaci babban lauyan gwamnatin kuma ministan shari’ah, Abubakar Malami da ya kalubalanci sahihancin dokar da ta sahalewa tsaffin gwamnonin karbar kudaden.

Idan dai za a iya tunawa, kungiyar SERAP ce ta shigar da wannan kara, inda ta bukaci wata oda daga kotun mai taken “Order of mandamus” a shekarar 2017.

Karar mai rijistar FHC/L/1497/2017, ta jaddada kudaden da suke karba ko kadan ba su da muhalli a kundin tsarin mulki da sauran dokokin da suka shafi aiki da ma’aikata.

Karar kungiyar ta samo sanadi ne bayan majalissar dokokin jihar Zamfara ta bayyana tsofaffin gwamnoni da mataimakansu za su lakume kimanin miliyan 700 duk shekara.

Akan wannan hujja, kungiyar ta bayyana kawo yanzu irin wadannan tsofaffin gwamnoni sun karbi kimanin biliyan 40, duk da cewar da yawa daga cikinsu sun zama Sanatoci ko Ministoci da suke karbar wasu kudaden daga gwamnati.

Dabo FM ta tattara cewa Kotu ta yanke hukuncin bukatarwar tsofaffin gwamnonin da su dawo da dukkan kudaden da suka karba.

Masu Alaka

Zamu yanke wutar da muke baku idan baku biya kudi ba – Najeriya ta fada wa Nijar, Togo da Benin

Dabo Online

Sadiya Umar Faruq ta karyata shafin Twitter da yace babu batun Aurenta da Shugaba Buhari

Dabo Online

Kotu ta kwace kujerar majalissa daga dan PDP ta bawa dan APC bisa rike shaidar zama dan kasar Birtaniya

Dabo Online

Lauya ya kai gwamnatin Najeriya Kotu bisa bukatar cire rubutun Ajami daga jikin Naira

Dabo Online

Kotu ta kori bukatar haramtawa Ibrahim Magu zama shugaban EFCC

Hassan M. Ringim

Kotun karar zaben shugaban Kasa ta yi watsi da karar kalubalantar nasarar Buhari

Dabo Online
UA-131299779-2