Siyasa

An umarci Buhari da ya kwace kudaden fanshon da aka bawa Kwankwaso da Shekarau


Wata babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a jihar Lagos, ta umarci gwamnatin tarayya da tayi amfani da ikonta wajen ganin ta karbo dukkanin makudan kudaden da tsofaffin gwamnoni wadanda suka rike mukaman Ministoci da Sanatoci kasar suka karba da sunan kudin fansho ciki har da Engr Rabi’u Musa Kwankwaso da Mallam Ibrahim Shekarau.

A lokacin da ta ke yanke hukunci, mai shari’ah Oluremi Oguntoyinbo, ta bukaci babban lauyan gwamnatin kuma ministan shari’ah, Abubakar Malami da ya kalubalanci sahihancin dokar da ta sahalewa tsaffin gwamnonin karbar kudaden.

Idan dai za’a iya tunawa, kungiyar SERAP ce ta shigar da wannan kara, inda ta bukaci wata oda daga kotun mai taken “Order of mandamus” a shekarar 2017.

Karar mai rijistar FHC/L/1497/2017, ta jaddada kudaden da suke karba ko kadan ba su da muhalli a kundin tsarin mulki da sauran dokokin da suka shafi aiki da ma’aikata.

Karar kungiyar ta samo sanadi ne bayan majalissar dokokin jihar Zamfara ta bayyana tsofaffin gwamnoni da mataimakansu za su lakume kimanin miliyan 700 duk shekara.

Akan wannan hujja, kungiyar ta bayyana kawo yanzu irin wadannan tsofaffin gwamnoni sun karbi kimanin biliyan 40, duk da cewar da yawa daga cikinsu sun zama Sanatoci ko Ministoci da suke karbar wasu kudaden daga gwamnati.

Dabo FM ta tattara cewa Kotu ta yanke hukuncin bukatarwar tsofaffin gwamnonin da su dawo da dukkan kudaden da suka karba.UA-131299779-2