Kiwon Lafiya

Rashin motsa jiki yana kisa irin na masu shan ‘Tabar Tabako’ da masu Kansa

A yanzu, rashin motsa jiki yana kawo asarar rayuka matuka kamar yacce masu shan taba suke mutuwa a fadin duniya.

DABO FM ta binciko wani bincike da masana kiwon lafiya a fannin cutar daji dake kasar Birtaniya suka gudanar akan tasirin da rashin motsin jiki yake wajen haifar da cutar daji musamman ta Mama dake damun mata yanzu.

A yayin binciken bayan kwarya-kwaryar binciken, sun gano cewa yakan haddasa cututtuka irinsu ciwon sigar, ciwon zuciya da kansar dake kama babban hanji.

Binciken da aka wallafa a mujallar Lancet, ya tabbatar da cewa kashi kaso 3 bisa 4 na mutanen da shekarunsu ya wuce 18 basa motsa jiki wanda bisa dalilin haka ake samu mutane miliyan 5.3 a kowacce shekara.

DABO FM ta tattaro cewa; a mutuwa 10 wacce cutar ciwon zuciya, ciwon siga da kansar hanji suka zama sanadi, guda 10 ciwon ya kamasu saboda rashin motsa jikinsu.

UA-131299779-2