//
Friday, April 3

Kudaden da ake bamu ‘basu taka kara sun karya ba’ – Sanata Shekarau

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Mallam Ibrahim Shekarau, sanatan Kano ta tsakiya a Najeriya, yace akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara yawan kudaden da take baiwa yan majalissun dokokin domin ayyukan mazabu.

Mallam Shekarau yace kudaden da yan majalissun dokokin Najeriya suke karba na ayyukan mazabu basu da yawa domin basu taka kara sun karya ba.

Ya alakanta rashin ganin ayyukan ‘yan majalissun da rashin karbar isassun kudaden da zasu aiwatar da ayyukan kwarai, kamar yadda sashin Hausa na BBC ya rawaito.

Ya kara da cewa dayawan yan Najeriya suna ganin cewar kudaden aikin mazabu yana shiga aljuwun yan majalissar ne wanda yace abin ba haka yake ba illa iyaka, aikin yan majalissun sun tabbatar da cewa an aiwatar da ayyukan da aka tsara yin aikin dasu ne.

Masu Alaƙa  Ina tsoron karawa da Kwankwaso - Shekarau

Ya kuma yi kira da gwamnatin tarayya da samar da hukumar da zata rika saka idanu ana kuma bibiyar ayyuka da aka tsara yi don ganin an cimma buri.

Daga karshe ya musanta zargin da ake yi wa majalissar kasar na zamewa bangaren zartarwa kamar rakumi da akala kan cewar duk abinda suka kawo, shi majalissar take tabbatarwa.

Ya bayyana cewa fahimtar juna ce ta sanya ba’a jin kansu.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020