Labarai

Yanzu-Yanzu: Jiga-jigen APC sun dira a Habuja da duku-duku kan shari’ar zaben Kano

Kafatanin shugabancin jam’iyyar APC na jihar Kano sun dira a babban birnin tarayya dake Abuja domin halartar shari’ar zaben gwamnan Kano da kotin koli zata yanke hukunci a gobe Litinin.

Majiyar Dabo FM ta hango jagorancin jam’iyyar na jihar Kano ciki har da kwamishinoni da masu bawa gwamna shawara sun isa Abujar sanyin safiyar Lahadi.

Tun dai bayan da kotun koli ta ta sauke gwamnan Imo gwamnonin da shari’ar su ke gaban kotun suka kadu da hukuncin, suka fara shige da fice ba dare ba rana domin ganin sunyi nasarar ci gaba da zama kan kujerun su.

Shari’ar dai da tafi jan hankali itace ta jihar Kano, tsakanin Abba Kabir Yusif na jam’iyyar PDP da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, sai shari’ar jihar Sokoto wadda ita ma tana cike da sarkakiya dalili da tazarar da gwamna Tambuwal ya bayar bai kai ko dari 400 wanda baifi yawan wani akwatun ba.

Gwamnonin Bauchi, Benuwai, Filato ma duk suna cikin wanda kujerar tasu take same take dabo.

Karin Labarai

Masu Alaka

Muna aiki ta karkashin kasa domin sasanta Sarki Sanusi da Ganduje -Shekarau

Muhammad Isma’il Makama

Zaben2019: Jihar Kano bata barayi bace – Ganduje

Dabo Online

Kai Tsaye: Daga Kotun sauraren karar zaben shugaban Kasa

Rilwanu A. Shehu

Ganduje ya bayar da tabbacin hukunta Gwamnan Ribas akan ruguje Masallaci da yayi

Dabo Online

Kano: Ganduje yana yunkurin rage darajar sarautar Sarki Sunusi

Dabo Online

Mun barwa Allah komai shiyasa hankalinmu yake kwance kan batun Shari’ata – Abba Gida Gida

Dabo Online
UA-131299779-2