(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

‘Yan Bindiga da dama a Zamfara sun zubar da makamansu tare da neman yafiya – Matawalle

Karatun minti 1

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya bayyana cewa adadi mai yawa daga cikin ‘yan bindigar jihar Zamfara sun watsar da makamansu.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a jihar ta garin Gusau ta hannun darkatan watsa labaran jihar, Yusuf Idris.

Ya bayyana cewa kawo yanzu, yan bindigar sun mika wuya ga gwamnatin jihar tare da ajiye bindigogi kirar AK47 sama da guda 200.

Yusuf Idris, da yake yiwa manema labarai kan ziyarar da tsohon shugaban kasa, Gen Yakubu Gowon ya kai fadar gwamnatin jihar dake garin na Gusau, yace gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake yiwa Gen Yakubu Gowon bayani.

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun mika wuya ga gwamnatin tare da yin alkawarin yin aiki da gwamnatin jihar wajen tabbatar da yakar matsalar rashin tsaro a jihar ta Zamfara.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog