0
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dake kasar Ingila ta doke takwararta ta Tottenham a wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar Turai na shekarar 2019.
Liverpool ta doke Tottenham da ci 2 babu ko daya ta hannun dan wasan ta Muhammad Salah da Divock Origi a mintuna na 2 da kuma 87.
Wannan ne karo na farko da Liverpool din ta dauki kofin tin bayan nasarar lashe kofin da tayi a shekarar 2005 a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
Tin dai a wasan da Liverpool ta buga da kungiyar Barcelona a filin wasa na Anfield, masu sharhi da hasashe suke ganin ta a matsayin kungiyar da zata iya lashe kofin a bana bisa irin bajintar data nuna na farko kwallaye uku da dora 1 a ragar Barcelona.
