Nabruska ya dakatar da fitowa a Fim din Hausa bisa nuna rashin goyon bayan kamun Sunusi Oscar

Shahararren dan wasan Barkwanci na masana’antar Kannywood, Mustapha Badamasi wanda aka fi sani da Nabruska ya bayyana ficewarshi daga masana’antar.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan kamun Sunusi Oscar, daya daga cikin Darakta a masana’antar Kannywood.

Nabruska ya bayyana cewa bazai sake fitowa a fim din Hausa ba har sai lokacin da wa’adin mulkin Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kare.

“Daga yau, na dakatar da yin Fim sakamakon abinda akayi na Sunusi Oscar 442.”

“Na fita daga cikin Kannywood har sai ranar da Allah ya kawo karshen gwamnatin jihar Kano.”

“Sakamakon abubuwan da suka faru da Sunusi Oscar 442, na dena fitowa a fina-finan Hausa.”

DABO FM ta binciko dai cewa a makon da muke ciki na tsakiyar watan Agusta, jami’an sukayi awon gaba da Darakta, Sunusi Oscar.

Inda daga bisani aka mika zuwa kotu, hukumar tace fina-finan jihar Kano ce take da alhakin kamun Sunusi Oscar.

Hukumar tace fina -finan dai ta zargi Oscar da sakin wasu wakoki ba bisa ka’ida ba, lamarin daya musanta zargin duk da cewa an aikata laifin da ake tuhumarshi da akan tin a shekarun baya.

Daga shafin Instagram, mutane da dama sun danganta kamun da akayiwa Oscan da cewa “Akwai saka Hannun Ali Nuhu a kan batun.”

Dabo FM bata tabbatar da hannu ko rashin Ali Nuhu a cikin lamarin ba.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.