LMC ta dakatar da Rabi’u Pele na Kano Pillars, wasanni 12 bisa yunkurin yiwa alkalin wasa dukan kawo wuka

LMC ta dakatar da dan wasan Kano Pillars, Rabiu Pele, wasanni 12 bisa yunkurin yiwa alkalin wasa dukan kawo wuka.

Hukumar LMC ta kama Rabi’u Ali Pele da karya dokar C1.3 da hukumar da tanada yayin da hukumar tace ta hukuta shi kamar yadda dokar C19 ta tanada.

Kamfanin dillancin Labarai na NAjeriya, NAN ya rawaito cewa; magoya bayan kungiyar ta Kano Pillars sun shigo filin tare da lalata allunan tallace-tallace da na’urorin gwaje gwaje.

Sun tayin jifa zuwa wajen kujerun VIP a yayin wasan da suke karawa da kungiyar kwallon kafa ta Rangers International wanda yaka taci canjaras 1-1.

Kalli Bidiyon abinda ya faru.
Masu Alaƙa  An samu raunuka da dama bayan farwa magoya bayan Kano Pillars a Katsina

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.