Anci tarar Kano Pillars miliyan 8 bisa janyo rigima ana tsaka da wasa a jihar Legas

Hukumar gudanarwar gasar Firimiya ta NAjeriya, taci tarar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tsabar kudi Naira miliyan 8, bisa rashin da’a da magoya bayanta sukayi yayin gudanar da wasansu a jihar Legas.

Salihu Abubakar, shugaban gudanarwar LMC, ya bayyana hukunci a wata sanarwar daya fitar sakamakon barkewar magoya bayan Kano Pillars cikin fili wasa, tare da hada hankalin mutane dama alkalan wasa.

‘Yan wasan Kano Pillars da magoya bayansu sun aikata laifin ne a wasa na 4 na Championship.

Dan wasa Rabi’u Ali Pele, ya karbi hukunci dakatarwa har tsawon wasanni 12.

Kamfanin dillancin Labarai na NAjeriya, NAN ya rawaito cewa; magoya bayan kungiyar ta Kano Pillars sun shigo filin tare da lalata allunan tallace-tallace da na’urorin gwaje gwaje.

Masu Alaƙa  Kano Pillars ta lashe kofin Aiteo na shekarar 2019

Sun tayin jifa zuwa wajen kujerun VIP a yayin wasan da suke karawa da kungiyar kwallon kafa ta Rangers International wanda yaka taci canjaras 1-1.

Haza zalika, hukunci yace Kano Pillars zata buga wasannin 3 batare da magoya baya ba a kakar wasanni ta badi tare da cire musu maki 3.

Hukumar ta bukaci Pillars ta karbi hukunci a kasa da awanni 48.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.