Labarai

‘Yan Bindiga a Zamfara sun kashe shugaban ‘Yan Banga

‘Yan Bindiga sun hallaka shugaban ‘yan bangar ne bayan kwanaki da suka dauka suna nemanshi a garin kauyen Rukudawa na karamar hukumar Zurmin jihar Zamfara.

Jaridar Leadership Hausa ta rawaito cewa maharan sun cimma shugaban ‘yan bangar, Rabi’u Mai Welda a dai-dai lokacin da yake yaben katangar gidanshi.

Jaridar tace Maharan sun shigo garin Rukudawa ne da rana tsaka dauke da manyan bindigogi tare da harbi sama.

Bayan shigarsu garin ne suka nufi gidan shugaban ‘yan bangar inda suke iske shi a saman katangar ta yake yabenta, su kayi masa umarni daya sakko, bayan ya saba umarnin sune take suka bude masa wuta.

Jaridar ta kara da cewa, duk da yanayin harbi da shugaban yasha, bindigar bata iya tasiri a jikinshi ba.

“Daga nan ne suka sakko da shi daga sama da karfin tsiya suka daure shi a bainar jama’a suka rika rotsa masa kai da sauke masa duwatsu a kai har sai da ya mutu.

Mutanen kauyukan Zamfara sun bayyana cewa magaran dake addabar mutanen jihar duk sun dawo cikin gari adalilin bamabamai da ake yi musu lugude a dazukan Zamfara din.

Bayan haka sun bayyana cewa maharan na da masu kai musu bayanan sirri a garuruwan suna masu kira ga gwamnati da su kara kaimi wajen ganin ganin sun bi sahun wadannan mahara domin gamawa da su.” – Leadership Hausa

 

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamnan Zamfara ya rike albashin ma’aikata 1,400 na tsawon watanni 30

Dabo Online

Sojoji sun tseratar da mutum 760 da akayi garkuwa dasu, sun kashe ‘yan bindiga 55 a Zamfara

Za’a gudanar da Zaben kananan hukumomi ranar 27 a jihar Zamafara

Dangalan Muhammad Aliyu

Wasu daga Sarakunan gargajiya na da hannu a rikicin arewacin Najeriya – Minista

Bana cikin taron hadin kan APC na ‘Babba-da-Jaka’ da Yari ya kira -Sanata Marafa

Muhammad Isma’il Makama

Mutum 42 sun rasa rayukansu a harin da ‘Yan Bindiga suka kai wasu kauyukan jihar Zamfara

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2