Labarai

Magidanci ya sauyawa ‘danshi suna daga Buhari zuwa Rabi’u Kwankwaso bisa ‘kasawar Buhari’

Salisu Matagwa, wani magidanci dan jihar Gombe n Najeriya, mai shekaru 45 a duniya, ya sauya sunan ‘danshi na cikinshi mai shekaru 9 daga sunan shugaba Buhari zuwa Rabiu Kwankwaso.

Salisu Matagwa, mazaunin unguwar Kumbiya-Kumbiya ta jihar Gombe, ya shirya taron nadin suna tare da gayyatar makota domin shaida sauyin sunan tare da yankan rago bisa tsarin addinin Islama, Jaridar Tribune ta tabbatar.

DABO FM ta tattara cewa mahaifin yaron ya bayyana jaridar cewa ya sauya sunan ‘dan nashi ne domin ya kubutar dashi daga jin kunya, wulakanci da suka daga wajen al’umma wadanda suke tunannin din da fari ya sanyawa dan nashi suna Buhari ne saboda shugaba Muhammadu Buhari.

Haka zalika ya bayyanawa jaridar cewa ya ‘sanyawa ‘dan nashi suna Buhari ne a dalilin Alhaji Salisu Buhari, tsohon shugaban Majalissar wakilan Najeriya, inda yace wasu mutane suna tunanin ya sanya sunan ne saboda shugba Buhari wanda har da kai ga ana masa lakabi da ‘Janaral’.

Mahaifin yaron ya shaida ya sauya sunan ‘dan nashi zuwa Rabiu Kwankwaso domin kubutar da danshi daga illar mutane da shugaba Buhari ya batawa a mulkinshi zasu iya yi masa.

Ya kuma nuna rashin jin dadinshi kan yacce shugaba Buhari yake tafiyar da tsarin mulkinshi inda yace ya sanyawa mutane wahala.

“Tin da yanzu mutane basa ganin mai kyau daga shugaba Buhari, na ce ya zama wajibi in canza sunan yaro na daga Buhari zuwa Rabiu Kwankwaso wanda a yanzu yake sananne duk fadin kasar. Ni masoyinshi ne na kwarai kuma ina goyon bayanci.

“Kwankwaso bai sanni ba. Bai bani kudi don sanyawa ‘dana sunanshi ba. Wannan rajin kaina ne. Don haka kada wanda yayi tunanin abinda nayi, sani akayi.”

“Ina da aiki na wanda dashi nake gudanar da rayuwata. Ba kudi nake nema daga wajen wani dan siyasa ba. Kawai dai Kwankwaso yana birge ni saboda gaskiyarshi.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Indiya: Mun samu Dalibanmu cikin koshin Lafiya da kwanciyar hankali – Kwankwaso

Dabo Online

Na saka kadarori na a kasuwa domin Ilimantar da Matasa a gida da kasashen waje – Kwankwaso

Dabo Online

Rikicin Siyasa: Ganduje ya sake gina Masallacin da Kwankwaso ya rusa

Muhammad Isma’il Makama

Sandar da Sabbin Sarakunan Kano suke rikewa “Kokara” ce – Kwankwaso

Dabo Online

Kwankwaso zai iya biyan kudin makarantar dalibai 370 daga cikin kudaden daya karba a majalissar dattijai – Bincike

Dabo Online

Hakki ne mu taru wajen Ilimantar da ‘ya yanmu don zama masu daraja in sun girma – Kwankwaso

Dabo Online
UA-131299779-2