Home LabaraiYanzun nan: Boko Haram sun afka garin Monguno, bayan janyewar Sojojin kasar Chadi

Yanzun nan: Boko Haram sun afka garin Monguno, bayan janyewar Sojojin kasar Chadi

by Dabo Online
0 comments

Kwanaki kadan bayan janyewar sojin kasar Chadi guda 1200 daga Najeriya, mayakan Boko Haram sun mamaye sansanin da Sojojin suka bari.

Jaridar The Cable ta rawaito cewar mayakan Boko Haram sun mamaye garin Monguno a jihar Borno.

Majiyoyi daga cikin jami’an tsaro sun shaidawa Jaridar cewar mayakan Boko Haram din sun fara aike da motoci zuwa sansani da misalin karfe 7 na yammar yau Talata.

Sai dai majiyoyin sun tabbatarwa da Jaridar cewa tini dai Sojojin kasa da takwarorinsu na sama suka fara shirin dakatar da yunkurin mayakan.

DABO FM ta tattara cewa mayakan Boko Haram sun afkawa garin ne cikin kasa da awanni 48 da Mallam Garba Shehu, jami’i a ofishin yada labaran shugaba Buhari yace babu matsala a yankin bayan janyewar dakarun kasar Chadi.

A cewar jaridar, majiyoyin sun tabbatar mata da cewa jami’an tsaro sun fara cin karfin mayakan na Boko Haram.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00