(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Sarki Sunusi ya tsige limami a Kano bayan ya bijirewa umarnin Sarkin Musulmi akan ganin wata

Karatun minti 1
Muhammadu Sunusi II
Muhammadu Sunusi II

Mai martaba Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sunusi II, ya tsige babban limamin masalacin Juma’ar Limawa a jihar Kano.

Masallacin yana unguwar Limawa ta karamar hukumar Kumbotso a cikin birnin jihar Kano.

Fadar mai martaba sarkin Kano ta zargin Mallam Salihu Muhammad da bijirewa umarnin Sarkin akan ganin watan sallar Idi.

Rahotanni sunce limamin bai ajiye azumi a ranar da Sarkin Musulmai ya bada sanarwar ganin watan ajiye azumin Ramadana ba har sai da ya kara kwana 1 bayan ganin watan da idanuwanshi kafin daga bisani yayi jagorancin sallar Idi a masallacin.

Tuni dai dakatarwar da Sarkin Kano yayiwa Mallam Salihu Muhammad ta fara aiki ba tare da bata lokaci ba.

Mai martaba Sarki ya bayyana cewa ba wannan ne karon farko da Mallam Salihu ya fara aikata wannan dabi’a ba, kuma masarautar ta gargadeshi akan hakan amma yayi kunnen kashi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog