‘Yan Bindiga sun hallaka mutane 10 a jihar Katsina

Karatun minti 1

Rundunar ‘yan sanda jihar Katsina ta tabbatar da rasa rayukan mutane 10 daga kayukan Guzurawa da Safana dake karamar hukumar Safana a jihar Katsina.

“Yan sanda sun tabbatar da alhakin kisan akan ‘yan ta’adda.

Rundunar ta sanar da haka ne a wata sanarwa data fitar ta hannun mai yada labaran ta, Gambo Isah a yau Laraba, 1/05/2019.

Yace yan bindigar sun shiga kauyukan ne da misalin karfe 6 na yamma akan babura 150 a jiya Talata. Nan ne suka fara gudanar da ta’adin nasu.

Ya kara da cewa, ‘Yan Bindigar sun kashe shanu dayawa tare da yin awon gaba da wasu shanun dama kayayyaki masu amfani da daraja na mutane bayan sun kashe mutanen.

Yace rundunar batayi kasa a gwiwa ba wajen kai sumame yankin da abin ya faru domin ceton mutanen garin.

Ya kuma bada tabbacin cewa hukumar tana bakin kokarinta wajen ganin ta kame ‘yan ta’addar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog