Majalissar Dattijai ta tabbatar da sake nada Emefiele a matsayin gwamnan CBN bisa kudirin shugaba Buhari

Majalissar dattawan Najeriya, ta aminta da bukatar shugaba Buhari na sake nada gwamnan bankin Najeriya, ‘CBN’ domin cigaba da jan ragamar bankin a shekaru 5 masu zuwa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, bayan kammala tantance Emefiele da kwamitin kudi da tattalin arzikin majalissar ya gudanar, shugaban majalissar Dr Bukola Saraki ya tabbatar da nadin kamar yadda shugaba Buhari ya bukata.

Majalissar ta baiwa kwamitin sati 1 domin gudanar da binciken tare da kammala shi.

Wa’adin Emefiele dai zai kare 2 ga watan Yunin 2019 hakan ya kawo karshen zangon wa’adin da kama aikinshi a shekarar 2014.

Sai dai tin bayan amincewar shugaba Buhari na sake nada Emefiele, masana tattalin arziki dama wadansu yan siyasa irin su Hon Gudaji Kazaure suke ganin Emefiele bai dace da cigaba da jan ragamar babban bankin ba.

Masu Alaƙa  CBN zata dauki dukkanin ‘yan jihar Ebonyi masu matakin ‘First Class’ a Economics aiki

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: