Ko dan darajar sunan Ali Nuhu dana sakawa ‘da na, bai kamata ya kaini Kotu ba – Zango

Fitaccen jarumin Kannywood, Adamu Zango ya bayyana rashin jin dadinshi bisa yacce jarumi Ali Nuhu ya kaishi gaban kotu.

Adam Zango yace lallai Ali Nuhu ya bashi kunya matuka, domin ‘dan daya fara haifa a duniya, sunan Ali Nuhu ya saka masa.

Zango ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da shashin Hausa na BBC, inda ya tataunawa da wakilinsu Nasidi Adamu Yahaya.

Zango ya amsa tambayar “Yaya kaji lokacin da akace Ali Nuhu ya kai ka Kotu?

Zango yace “Da sammaci yazo, na tura masa sako nace wallahi ka bani kunya.”

“Ina ganin cewa inada dangi sama da mutum 500, amma na haifi ‘da na na farko na saka sunanka, ai ko darajar wannan bai kamata kace ka turo min wannan abin wai ka kaini Kotu ba.”

Domin Kallon cikakkiyyar hirar danna bangon kasan wannan rubutun

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.