Majalissar Bauchi ta kaddamar da dokar hana tilasta dawo da kudaden da masu mulki suka sace

Karatun minti 1

A lokacin da yake kasa da makonni biyu ga karewar wa’adin mulkin gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abubakar, ranar Laraba, majalissar jihar Bauchi ta kaddamar da dokar hana bincike ko tilasta dawo da kudaden da masu mulki suka sata a jihar.


Jaridar Punch ta rawaito cewa daga cikin kudirorin da majalissar ta rattabawa hannu ta hada da karin hakimai da dagatai, dokar hana rufe manyan hanyoyin zuwa kauyuka da wasu wuraren a cikin gari.


Kudurorin da mataimakin masu rinjaye, Hon Abdullahi Abdulkadir, mai wakiltar Bura, ya gabatar a majalissar wanda ya samu goyon bayan Hon Sale Nabayi na Ganjuwa da Hon Magaji Inuwa na Jama’are.

Kudurin hana tokare manyan hanyoyi ya samu shiga ta hannun shugaban masu rinyaje a majalissar Tijjani Aliyu da goyon bayan Hon Yunusa Ahmad na Warji.

Kudirin dokar ya samu karatu 3 a lokaci daya, ranar Laraba da shugaban Majalissar ya jagorancin kudirin.


Shugaban Majalissar, Kawuwa Damina, wanda ya karanto kudirin yace dukkanin kudirorin wanda yace ya samu amintar dukkanin ‘yan majalissu 13 daga cikin 31 da suka halarci zaman na Laraba.


Ya kara da cewa; a bisa bukatarwar mutane da tabbatar da wannan kudiri, suna fatan gwamnan bazai yi sanya wajen saka hannu a sabon tsarin ba.

A jawabin dan majalissar Lere/Bula ya ce shugaban majalissar ne kadai yake da dalilin tabbatar da kudirin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog