Home LabaraiMajalissar Dokokin jihar Bauchi ta tantance Kwamishinoni 20

Majalissar Dokokin jihar Bauchi ta tantance Kwamishinoni 20

by Rilwanu A. Shehu
0 comments

Majalissar Dokoki ta jihar Bauchi ta tantance kwamishinoni 20 cif, kamar yadda Gwamnan jihar Alh. Bala Muhammad ya aike mata, a watan da ya gabata.

Kakakin majalissar dokoki ta jihar, Rtd. Hon. Abubakar Y Sulaiman ne ya jagoranci tantancewar a zauren majalissar dake birnin Yakubu.

Kwamishinonin dai guda 20 ne, kamar yadda Gwamnan ya tura da sunayen su a watan da ya gabata.

Hakan ya bayyana cewa kowacce karamar hukuma a jihar ta samu Kwamishina.

Tun a ranar Talata 3 ga watan Satumba ne majalissar ta fara zaman tantancen kwamishinonin, a jiya Laraba kuma ta kammala tamtance su baki daya.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00