Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da kama wasu malaman addinin Musulunci guda biyu biyo bayan keta dokar hana fita da sukayi.
Gwamnatin tace malaman su jagoranci sallar Juma’a duk kuwa da dokar da gwamnatin ta saka na hana fita da haramta hada taron da jama’a zasu hadu.
Da yake bayyana kamun, Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida yace gwamnatin ta kama Mallam Aminu Umar Usman da Mallam Umar Shangei.
Kwamishinan ya kara da cewar manyan malaman jihar sun bayar da shawarar rufe masallatan Juma’a wanda gwamnati ta dauki hukuncin dokar hana fita, sai dai yace duk malamin sun ki bin dokar.
A sanarwar da kwamishinan ya fitar a shafinshi na Twitter, yace za’a gurfanar da malaman guda biyu a gaban kotu.
