Labarai Taskar Malamai

Manzon tsira SAW yayi umarnin rufe fuska, wanke hannu tin kafin annobar Coronavirus – Sheikh Hamza

Sheikh Hamza Uba Kabawa, babban limamin masallacin kasuwar Singa ta jihar Kano yace Manzon Allah SAW ya bayyana matakan kariya daga annoba tin kafin zuwan Coronavirus.

A hudubar da malamin ya gabatar a jiya Juma’a, shehin malamin yace matakan kariya da suka kunshi rufe fuska da sanya safar hannu a yayin da ake mu’amala a lokacin annoba.

A Hudubar da DABO FM ta halarta, malamin ya kumayi kira ga ‘yan kasuwa da su sassauta farashin kayyaki musamman na abinci domin saukakawa al’umma.

Ya kuma gargadi ‘yan kasuwar akan dabi’ar da yace sunayi na boye kayayyaki amfani domin jiran suyi tsada kafin a fito da su a siyarwa da al’umma.

A wani dan kwarya kwaryar bincike da DABO FM tayi, ta gane cewar ana siyar da ‘Face Mask’ a kan kudi na N300-500 wanda a satin da ya gabata bata fi N20 ba.

Daga ciki, akwai na yadi sa ake siyar da su kan N100-150 a lokutan bayan, yanzu ana siyar da su a kan N1000.

Karin Labarai

Masu Alaka

Yi wa Mata kaciya ba Addini bane, muguwar Al’ada ce kuma cutarwa ne -Sheikh Gumi

Dangalan Muhammad Aliyu

A guji yada jita-jita: Sheikh Dahiru Bauchi bai zagi Buhari akan rufe iyakoki ba

Dabo Online

Zagin Shuwagabanni da Malaman Addini tamkar zubar da jini ne – Dr Rijiyar Lemo

Dangalan Muhammad Aliyu

Allah Ya’azurtani da samun ‘Ya’ya 70 da tarin Jikoki – Sheikh Dahiru Bauchi

Dabo Online

Malamai masu halin Yahudawa sune kullin suke kallon kuskuren mutum ba alkairinshi ba – Dr Gumi

Dabo Online

Yunwa, Talauci, Tashin hankali da bala’i kawai ake fama dashi a Najeriya – Sheikh Muhd Nasir

Dabo Online
UA-131299779-2