Masalissar jihar Kano ta tabbatar da karin Manyan Sarakuna 4

A zaman majalissar jihar Kano na yau Laraba, majalisssar ta tabbatar da kudirin samar da manyan masaurautu 4 a jihar.

Kudirin da aka gabatar da a gaban Majaliisar ranar Litinin, ya samu karatu na farko ranar Talata.

‘Babu wani mai hamayya da kudirin a cikin majalissar lokacin da aka sakawa dokar hannu, saboda duk wadanda basu amince da dokar ba sun fice daga zauren majalissar.’

“Lallai Gwamna yanaso yayi duk mai yuwuwa wajen karya darajar Sarki Sunusi bayan da ya zarge shi da goyon bayan Abba Kabir Yusuf a takarar gwamnan ihar Kano – Cewar wani dan majalissar daya bukaci a sakaaye sunanshi.

Tin da safiyar yau ne gwamna Ganduje ya bayyana cewa da zarar kudirin ya zo gabanshi zai rattaba masa hannu.

%d bloggers like this: