‘Yan Bindiga sun yanka mai unguwa a jihar Sokoto, sun harbe ‘dan sanda 1

‘Yan Bindiga sun yanka mai unguwar garin Balle dake karamar hukumar Gudu a jihar Sokoto.


Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa wasu mutane su 10 a kan babura, sun fito da mai unguwar suna jan shi har ta kai ga sun yanka shi.


Wani daga cikin mutanen garin ya rubuta cewa; ‘Yan bindigar sun afkawa garin Balle, gari da yake mai zaman lafiya a karamar hukumar Gudu ta jihar Sokoto.


“Sun shigo sun kashe mai unguwa, Sarkin Yamman Balle, bayan sun fito dashi daga cikin gidanshi.”


“Du ba da yadda suka kai wa ofishin yan sanda hari bayan sun harbe wani jami’in dan sanda, sun kone motoci, mutum zai iya cewa wadannan mutane suna amfani da gazawar jami’an tsaro.”

Masu Alaƙa  Anyi yunkurin harba makamai masu linzami a birnin Makkah da Jeddah.


“Tsakanin gidan mai unguwar da ofishin ‘yan sandan bai muce mita 500 ba.”


Sai dai har yanzu yan sanda basu ce komai akan lamarin ba, har lokacin da muka hada wannan rahotan.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.