Masu garkuwa da mutane sun kashe turawa a jihar Kaduna

Karatun minti 1

Shashin Hausa na BBC ya rawaito cewa masu garkuwa da mutane sun hallaka turawa biyu a jihar Kaduna.

Rohotan yace ‘yan bindigar sun kashe turawan ne a wani wajen shakatawa dake Jihar ta Kaduna.

“Ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya ya tabatar da aukuwar lamarin, wadda kungiyar da ta ke wa aiki ta bayyana cewa sunanta Faye Mooney.

Kungiyar mai suna Mercy Corps ta ce Faye Mooney na aiki ne a Najeriya, kuma abin takaici ya faru a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka far ma wurin da ta ke hutunta a jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

‘Yan sanda a jihar ta Kaduna sun tabbatar da mutuwar wani dan Najeriya, bayan sace wasu mutum uku da maharan suka yi a ranar Jumma’a.” – BBC Hausa

Batun satar mutane don biyan kudin fansa ya dade da zama ruwan dare inda ta kai ga har satar mahaifiyar Gwamnan jihar Katsina, Mallam Aminu Bello Masari.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog