Labarai

Sarkin Zurmi na Zamfara ne yace a kashe dukkan mutanen Dumburum – Gov Abdul’aziz Yari

  • “Sama da shekaru 3, Dumburum ta kasance wata matattarar kuma maboyar ‘Yan Bindiga, Sarkin Zurmi ya taba cemin a kashe dukkanin mutanen kauyen saboda duk ‘Yan ta’adda ne.”
  • “Nayi mamaki danaji majalissar Sarakunan Zamfara sunce hare-haren da sojojin sama suka kai a kauyukan Dumburun mutane kawai yake kashewa.” – Gov Yari.

Gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya bayyana cewa akwai wata rana da Sarkin Zurmi ya taba ce masa aje a kashe duka ‘yan kauyen Dumburum bisa dalilin kasancewar kauyen maboyar ‘yan bindiga sama da shekaru 3.

Jaridar Sahara Reporters tace Gwamna Yari ya bayyana haka ne bayan tarbar Kwamitin masu bincike kan ikirarin da Sarakunan Zamfara sukayi na cewa hare-haren sojojin sama na kashe mutanen gari ne kawai.

Gwamna Yari yayi martani da cewa gwamnati bazata bada hakuri ko nuna kulawa kan maganar da Sarakunan sukayi ba, yace Sojojin saman da suka kai hari sun tabbatar da cewa maboyar ‘Yan ta’addar suka tarwatsa lokacin harin.

“Iya masaniya ta,  kuma a matsayina na shugaban jihar Zamfara, banga wani laifi ko aikata abinda ba dai dai ba a harin da sojoji sukayi; kuma har yanzu bamu samu labari akan an kashe mutanen gari ba.” – a cewar Gwamna Yari.

“Nayi mamaki dana ji hadda Sarkin Zurmi a wadanda suke cewa an kashe mutanen gari a harin sojojin saman, shi da kanshi ya taba cemin Dumburum mattara ce ta ‘yan bindiga don haka ya kamata a tashi kauyen baki daya.”

“Bazamu kyale wasu mutane da suke zamansu a Abuja su ƙirƙiri abinda zai hana sojoji cigaba da yaki da ‘yan ta’addar ba.”

“Ina kira ga dukkanin jami’an tsaro musamman sojojin sama, da su cigaba da gudanar da aikinsu na dawo da zaman lafiyar da jihar Zamfara ta rasa tin shekarar 2007, zamu basu dukkanin wani taimako da goyon baya wajen cigaba da aiyukan nasu.”

“Ku cigaba da luguden wutar da kukeyi domin nunawa ‘yan ta’addar cewa akwai gwamnati a ban kasa, kuma bazamuyi zaman sulhu dasu ba saboda mun taba yin hakan dasu, suka nuna mana sun dena kuma zasu bawa yaransu umarnin denawa, amma sai yaran suka cigaba da yin ta’addancin.

Idi Lubo, shugaban wakilan masu binciken, ya baiwa Gwamna takardar ta’aziyya wacce shugaban rundunar Sojin Sama, Sadique Abubakar ya aikowa Gwamna Yari, inda ya tabbatar masa da zaiyi duk mai yiwuwa wajen gano gaskiya akan kashe-kashen Zamfara.

Kwamitin masu bincike ya samu ziyartar wasu jami’an tsaro, ma’aikatan Gwamnati tare da sarakunan gargajiya.

Karin Labarai

Masu Alaka

Jama’ar gari ne kadai suke mutuwa a harin Jiragen Sojoji a Zamfara

Dabo Online

Zamfara: Gishirin Lalle yayi sanadiyar mutuwar mutum 14

Muhammad Isma’il Makama

Ana ta Rai…: Majalissa dokoki ta aminta da karin sabbin masarautu a jihar Zamfara

Dabo Online

An saukar min da wahayi zanyi shugabancin Najeriya -Yariman Bakura

Muhammad Isma’il Makama

Shugaba Buhari ya dakatar da hakar “Gwal” a jihar Zamfara

Dabo Online

PDP, NRM sun lashe dukkanin kujerun mulki na jihar Zamfara a karon farko

Dabo Online
UA-131299779-2