President Donald Trump
Labarai

Masu ruwa da tsakin Shari’a 500 sun sanya hannu a takardar bukatar tsige Donald Trump

A ranar juma’a ne wasu masana shari’ah a kasar Amurka suka rattaba hannu akan wata wasika da ta bukaci majalissun kasar da su yi kokarin tsige Donald Trump akan laifukan da ya tafka da suka shafi zaben kasar a shekara mai zuwa.

Masanan da suka kai 500 sun bayyana cewar cin amanar kundin tsarin mulki ce, gami da sabawa dokar ofishin shugaban kasa, ace an yi amfani da wata dama don bukatar wata kasa ta sa baki akan zaben Amurka don bukatar mutum daya kawai.
Sun kara da cewar bayar da damar kasar Ukraine ta yi kutse cikin sabgar zaben Amurka ba karamin ganganci da hatsari gami da haifar da kaskanci ga kasar.

Wannan dai wasika na zama tamkar karawa dabe makuba ne, bayan wasu masana shari’ah hudu sun bayyana a gaban kwamitin shari’ah na majalissar dokokin kasar don samun karin haske daga garesu. Inda mutane uku suka yi Allah-wadai da yunkurin na Trump. Daya kuma ya nuna ba wata matsala akan hakan.

Masanan dai da suka futo daga manyan jami’oi a kasar, kamar na yankin Yale, Columbia da Rutgers, sun fadada cewar bayanai da suka futo daga bakunan mukaddashin shugaban ma’aikatan fadar Trump, Mick Mulvaney, gami da lauyan Trump Mr. Rody da su jakadan Amurka a Ukraine Bill Taylor, ababen sa shakku da tayar da hankali ne. Kuma dole a dauki lamarin da muhimmanci.

Daga karshe suka jaddada cewar majalissun Amurkan ba su da wani tasiri ko ikon aminta ko akasin haka akan duk wani batu da kundin tsarin mulki ya gama yin bayaninsa. Akan hakane suka bukacesu da su yi abin da ya kamata kamar yanda mutanen da suka gabacesu suka aikata wajen martaba kundin tsarin mulki.

Masu Alaka

Fitaccen mai shirya bidiyo a kasar Koriya ta Kudu ya karbi Musulunci ta sanadiyyar ‘Youtube’

Dabo Online
UA-131299779-2