Labarai

Za’ayi bikin radin sunan wani matashi daya chanza sunanshi zuwa Muhammadu Buhari a Kano

A kalamin irin na ko da me kazo an fika, a jihar Kano, kungiyar wasu matasa masoya shugaba Muhammadu Buhari, sun shirya gagarumin chanjin sunan wani dan kungiyar.

A wani hoto dake yawo a kafar sadarwar wacce sashin Hausa na Legit.ng ta fitar, mai dauke da goron gayyata zuwa wajen chanjin sunan, matasan sun kira kansu da “Matasa dake zaune akan titin gidan Zoo, Masoya shugaba Muhammadu Buhari da gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai basu bayyana ainahin sunan matashin wanda yayi ra’ayin sauya sunanshi zuwa Muhammadu Buhari.

DABO FM ta shaidawa idanuwanta ganin goron gayyatar wanda aka tsara gudanar da radin sunan a ranar Lahadin 8 ga watan Disambar 2019 da misalin karfe 4 na Yamma.

Za dai a gudanar da bikin a makarantar Firamare ta Wada Kura Science kusa da Makarantar Sakandire ta Ado Gwaram a unguwar Zoo Road dake jihar Kano.

UA-131299779-2