Ganduje na shirin ayyana Sarkin Bichi a matsayin babban sarki a Kano

Bayan samun nasarar da Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yayi na sahalewar sabuwar dokar masarautu da majalisar jihar Kano ta zartar akwai yiwuwar gwamnan ya zabi Sarkin Bichi a matsayin shugaban majalisar sarakuna ta jihar Kano.

Kafar Dabo FM ta jiyo jaridar PremiumTimes na furta hakan da sanyin safiyar Asabar, bayan wato tattaunawa da gwamnan yayi da kafar yada labarai ta ChannelsTV.

Ganduje dai ya bayyana cewa yana dab da ayyana shugaban majalisar sarakuna ta jihar Kano nan gaba kadan.

Wata ziyara ta musamman da gwamnan ya kaiwa Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero da yammacin ranar Juma’a na daya daga cikin abinda ke karfafa wannan magana ta cewa ‘yar manuniya ce ta zabar sarkin na Bichi a wannan matsayi.

Masu Alaƙa  Bata-garin mabiya Kwankwasiyya sun yi wa Sheikh Pantami ihun ‘Bamayi’

Sabuwar dokar masarautu dai ta damkawa gwamna wuka da nama nadamar zabar shugabancin sabuwar majalisar sarakuna ta jihar Kano.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.