Amana: Wa’adin aikin CP Wakili ‘Singham’ yazo karshe

Kwamishan ‘yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakili, ya ajiye aikin dan sanda a ranar Juma’a data gabata 24/05/2019.

Wakili ya ajiye aikin ne bisa cikarshi shekaru 60 a duniya, lokaci ne da dokar gwamnati ta gindayawa dukkanin ma’aikacinta ajiye aiki.

CP Wakili, dan sanda ne da yayi shura wajen rike aikinshi bisa amana tare ta tabbatar da aikin doka akan duk wanda ya ketare dokar.

Yayi shura wajen yaki da sha, siye da siyarwar miyagun kwayoyi, bisa jajircewar aikinshi a jihar Kano, al’umma suka sanya masa suna “Singham”, sunan wani shirin fim din kasar Indiya, mutane suna ganin dama kamar anyi fim dinne don nuna ayyukan Wakili.

Wakili ya kasance dan sandan da ba’a taba irinshi ba, domin shine dan sanda kuma ‘Celebrity’, wanda takai duk manema labarai da kamfanunuwan labarai ya zama shine ”Babban Labarinsu.”

A lokacin gudanar da zaben Najeriya na 2019, CP Wakili ya kasance ‘dan sandan da Najeriya tafi ambata bisa jajircewarshi ta hana magudi da tabbatar da tsara a jihar Kano.

Wasu daga cikin manya ayyukan CP Wakili a Lokutan Zabe

%d bloggers like this: