Labarai

Tarauni: Hanan Buhari zata kaddamar da koyar da mata 100 ilimin daukar hoto wanda dan majalisa ya dauki nauyi

Dan majalisa mai wakiltar Tarauni, Hafizu Kawu ya dauki nayin mata 100 domin koyon ilimin daukar hoto wanda Hanan Buhari zata kaddamar a karamar hukumar Tarauni.

Dabo FM ta zanta da daya daga cikin hadiman gidan dan majalisar, Sen Abba Madugu, wanda ya tabbatar da faruwar hakan ya kuma yi mana karin haske akan kabakin arzikin da Hafizu Kawu zai kawo karamar hukumar Taraunin.

Madugu ya ce “Ranar Asabar an gudanar da taron shirye shiryen daukar nauyin mata 100 wanda Hafizu Kawu ya dauki nauyi a Marshal Event Center dake kwanar sabo a karamar hukumar Taraunin jihar Kano.”

“Kuma nan gaba kadan yar gidan Shugaba Muhammad Buhari, Hanan Buhari ce zata zo ta kaddamar da daukan nauyin mata darin.”

Hanan Buhari kwararriyar mai ilimin daukar hoto ce wadda ta samu shaidar digiri da maki mafi daraja a wata jami’a dake Birtaniya, yan kwanaki kadan da suka gabata an gano hotunan zuwan ta jihar Bauchi cikin jirgin saman fadar shugaban kasa wanda hotunan sun yamutsa hazo a dandalin sada zumanta.

Karin Labarai

Masu Alaka

Nayi Tir da shigar tsiraicin da Rahama Sadau tayi -Mai Sana’a

Muhammad Isma’il Makama

Sarki Sunusi ya tsige limami a Kano bayan ya bijirewa umarnin Sarkin Musulmi akan ganin wata

Dabo Online

Zan bi tsarin aiki ko za’a kashe ni – Kwamishinan zaben jihar Kano

Dangalan Muhammad Aliyu

Bata-garin mabiya Kwankwasiyya sun yi wa Sheikh Pantami ihun ‘Bamayi’

Dabo Online

Hisbah ta aika sammaci ga baturiyar Amurka da matashin da suke kokarin aure a Kano

Muhammad Isma’il Makama

Kano: Mutane 176 ne suka rasa ransu sakamakon hadarin jirgin sama a rana irin ta yau

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2