Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu kan aminta da gina katafaren sabon filin tashi da saukar Jiragen sama a jihar Ebonyi.
Hakan na zuwa ne bayan da gwamnan jihar, David Umahi ya mika koko zuwa ga gwamnatin tarayyar domin a gina wa jihar sabon filin Jirgin.
Minitsan harkokin sufurin sama, Hadi Sirika ne ya bayyana sanya hannu don fara ginin sabuwar tashar da shugaba Muhammadu Buhari yayi a wata wasika da ya aikewa gwamna Umahi.
Takarda da Daraktan kula bangaren kare inganci na ma’aikatar, T.A Alkali ya sanyawa hannu a matsayin Ministan harkokin jiragen sama ya bayyana cewa; hukumar ta bada damar yin filin Jirgin ne bayan ma’aikatanta sun kai ziyarar duba chanchantar filin da aka bayar domin yin tashar jiragen.
“An umarceni da in bayyana maka Izinin da Ministan harkokin sufurin sama ya bayar na gina katafaren filin tashi da saukar jirage ta duniya mallakin jiha wacce a filin da aka duba.”
