Matsanancin zafi ya fara hallaka mutane a kasashen Turai

Karatun minti 1

Tin bayan ficewa daga yanayin hunturu, kasashen Turai suka shiga cikin matsanancin zafin da akayi shekaru aru aru ba’a ga irin yanayin a nahiyar ba.

DABO FM ta binciko yacce rayuwa take wahala da kunci ga mutanen dake rayuwa a nahiyar Turai kasancewarsu ma’abota yanayin hunturu kusan ko da yaushe.

Binciken DABO FM ya gano cewa a kasar Switzerland, mutane basa siyan na’urar sanyaya wurare ko fanka saboda dalilin rashin yin kakar zafi a kasar.

Bincikenmu a birnin Geneva na nuna cewa kasar tana kasancewa a yanayin ma’aunin 15-20°C a matsayin yanayin da akeyi bayan hunturun sanyin kasar da akeyi daga -7°C zuwa 5°C. A yanzu anayin zafi a kasar akan ma’aunin 37-39°C.

Rahotanni daga kasar sun tabbatar da al’ummar kasar Switzerland a yanzu suna lekawa kasar Portugal makwabciyar kasar domin siyan fankoki.

A kasar Spaniya, rahotanni sun bayyana yacce al’umma suke rasa rayukansu dalilin matsanancin zafin akan ma’aunin 40°C.

Jaridun kasar a ranar Juma’a, sun rawaito mutuwar wani saurayi mai shekaru 17 na haihuwa ya rasa ranshi dalilin matsanancin zafi.

“Matashin ya fara jin jiri, lamarin daya sanya shi fadawa tafki domin neman sanyi don yaji dadin jikinshi.”

“Fitowarshi ke da wuya ne, ya faɗi” – Kamar yadda gwamnatin Kudancin Andalusiya ta tabbatar.

ANyi gaggawa tafiya dashi zuwa asibitin Cordoba, inda a nan ne yace “Ga garin kunan”.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog