Engr.-Muazu-Magaji-Dan-Sarauniya
Labarai

Tsohon kwamishinan Kano, Muazu Magaji ya caccaki gwamnatin tarayya

Tsohon kwamishinan ayyuka da tsara birane na jihar Kano, Muazu Magaji Dan Sarauniya, ya caccaki gwamnatin tarayya.

Tsohon kwamishinan ya yi martanin ne bayan da gwamnatin tarayya ta yi kakkausan martani ga Gamayyar Kungiyoyin Arewa akan furucin gazawar gwamnatin tarayya bayan karuwar munanan hare-haren ‘yan Binduga da mayakan Boko Haram a jihohin Arewa.

DABO FM ta tattara cewar gwamnatin ta ce wa kungiyar sun ci sa’a sun yi kalamansu a lokacin mulkin Dimokradiyya.

Sai dai a nashi martanin, Injiya Mu’azu Magaji ya ce gwamnatin tarayya ta ci sa’a mutane sun zabe ta wanda har ya kai ta ga darewa kan karagar mulki.

“Kunyi sa’a mun zabe ku, kun hau kujerar da yanzu ku ke takura da nakastamu.”
Daga shafin Facebook na Muazu Magaji – Tsohon Kwamishinan ayyuka na jihar Kano.

A ranar 18 ga watan Afrilu 2020, tsohon kwamishinan ya yi kalaman ‘farin ciki’ ga mutuwar shugababn ma’aikatan gwamnatin tarayya, Mallam Abba Kyari da ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Kwabid-19.

Sa’o’i kadan bayan furucin, gwamnan Kano, Dr Abdullahi Ganduje ya sauke shi daga mukamin kwamishina a jihar Kano.

Cikin kasa da kwanaki 30, Muazu Magaji ya kamu da cutar Kwabid-19, in da tayi tsanani har sai da aka sanyashi a dakin masu matsananciyar rashin lafiya.

Karin Labarai

UA-131299779-2