Mijin da matarshi ta caccakawa wuka ya bayyana hujjojin ture-turen hotunan batsa da takeyi da samarinta

dakikun karantawa

Sa’eed Muhammad mijin da matarshi ta caccakawa wuka yayin taron manema labarai inda ya bayyana hujjojin daya dogara dasu na cewa matar tashi tana cin amanarshi.

Sa’eed ya nuna hotunan da bidiyo tare da sakonnin karta kwana a kan manhajar Instagram da Twitter wanda takeyi da samarin ta, hadi da tura musu hotunan banza, a cewar Sa’eed.

A dai dai lokacin da Sa’ees yake nunawa manema labarai bidiyon rawar da Hanan takeyi yace “Gashinan abubuwan da takeyi, rawar a cikin daki a gidana, idan tayi rawa ta batsa sai ta turawa samarinta.”

https://twitter.com/dadiyata/status/1148203879982620674?s=21

Bayan ture-turen hotuna da bidiyo na batsa da Sa’eed ya ce matarshi Hanan tanayi, ya kara da cewa Hanan tana shaye-shaye inda a cewarshi yace ya kamata sau tari tana ta’ammali da kayan maye wanda shima ya wallafa bayyana hujjojinshi akan shaye shayen da takeyi.

DABO FM ta binciko daga cikin wadannan hotuna da Sa’eed Hussain ya nunawa duniya wanda acewarshi yayi ne domin tsira da mutunci bisa zarginshi da akeyi na lakadawa matarshi dukan kawo muka.

Sai dai DABO FM zata iya wallafa hotunan sakonnin da Sa’eed yace Hanan ce takeyi da samarinta saboda cin karo da ka’idojinmu bisa addinin Islama.

Sai dai binciken mu yakai ga dubo suwaye wadanda sunayensu ya fito a matsayin wadanda Hanan din take magana dasu.

Sa’eed Muhammad Hussain ya kara bayyana cewa a dai dai lokacin daya kakkama Hanan da dabi’ar shaye shaye da ture-turen hotuna da bidiyo na batsa ga samarinta, yana fadawa iyayenta game da hakan.

Ya kara da cewa har ta kai ga su dunguma wajen babban limamin masallacin Al-Furqan dake jihar Kano duk dai domin ayi mata fada da nasihohin addinin musulunci dana rayuwa ko zata gyara ta dena abinda takeyi.

Sauran na zuwa…..

Karin Labarai

Sabbi daga Blog