Da suwa Hanan take tarayya wajen ture-turen hotuna da maganganin batsa?

dakikun karantawa

Tin bayan bayyanar lamarin da aka zargi Fatima Musa (Hanan) da caccakawa mijinta Sa’eedu Muhammad, wuka a ciki, al’umma da dama sun magantu akan batun.

Daga bangaren masu fafutukar kare hakkin mata, sun bayyana lamarin a matsayin ”Kare kanta daga jubgar Sa’eed ne ya saka Hanan ta caccakawa Sa’eed, wuka a ciki.”

To sai dai bayan farfadowar Sa’eed, ya fito ya bayyana hujjojinshi daya ce yana dasu na cewa bai daki Hanan ba, hasalima itace ba lokacin caka wukar bane yunkurinta na farko wajen hallaka shi ba.”

Ya bayyana hujjojin da suka hada da sakonnin batsa da hotuna wadanda take turawa samarinta na waje.

Binciken DABO FM ya bi dindigi wajen binciko sunaye da kuma hotunan wadanda ake zargi dayin tarayya da Fatima Musa duk da sunsan cewa matar aure ce.

Daga cikin wadanda ake zargi da magana da Hanan duk da tana da aure, akwai masu amfani da manhajar Instagram masu suna @Habib4u da @6affa.

DABO FM ta shiga manhajar Instagram don neman masu sunaye da hotunan suka nuna dasu Hanan take magana duk da tanada aure.

DABO FM ta fara binciken ta akan @Habib4u a shafin Instagram, inda wakilanmu suka bincika sunanshi Ahmad Habibu.

Bayan shafe binciken mu akan shafin @Habib4u, a dai dai lokacin bincikenmu, yana da mabiya 1,231 inda shi kuma yake bin 2,032.

Daga cikin wadanda Ahmad Habibu @Habib4u yake bi tare da suma suna binshi, sama da kaso 70-80 dukkanin su mata ne.

Sai dai a daidai lokacin da muka hada wannan rahoto, mun samu cewa, tini dai aka chanza hoton da yake kan farfajiyar mai shafin tare da mayar da shafin ‘Private’ (Babu wanda zai iya ganin abinda ya kunshi shafin sai mai shafin ya yarda tare kuma da goge hotuna 121.

Hakan yasa muka tabbatar da cewa mai amfani da sunan @Habib4u a manhajar Instagram dattijon mutum ne, DABO FM ta gano yacce ‘yan mata suke tururuwa zuwa shafin bisa dalilin kaso 70-80 da suke bin shafin dukkaninsu mata ne.

Daga daya bangaren kuma na suna @6affa duk dai a shafin Instagram, binciken DABO FM ya tabbatar da cewa tini dai mai wannan shafin ya gogeshi ko chanza suna don kar a gane shi.

Kafin rufe shafin @6affa, yana da mabiya 5,726 kamar yadda shafin Piknu, Ingrampro da Picdeer suka nuna a cikin kudin bayanan su.

@6affa yana amfani da sunan GENERAL kafin ya goge shafinshi a Instagram inda kuma yake amfani da sunan Alïyu⚡ (@alieyu_jr) El Mejor a manhajin Twitter, wanda shima ya rufe shi.

Sai dai duk da haka DABO FM ta tsaurara bincike wajen bankado wani hotanshi da google ya ajiye kafin kammala gogeshi daga kudinta dake tattara dukkanin abubuwan da suke yawo a kafar Intanet.

Shafin Piknu ya bayyana wannann hoto a matasyin hoton 6affa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog